Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewa, Ayatullah Nuri Hamedani yayin da yake yin tir da hare-haren baya-bayan nan da gwamnatin Sahayoniya mai kashe yara ta kai wa Lebanon, ya jaddada cewa: "Ya zama wajibi dukkan Musulmi da masu neman ’yanci a duniya su dauki matsaya mai ƙarfi kan wannan hari da wannan laifi, tare da bayyana cikakken goyon bayansu ga al’ummar Lebanon, musamman ga Hizbullah mai daraja.
Ga cikakken saƙon nasa kamar haka:
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai
Manyan hare-haren da gwamnatin Sahayoniya ta kai a Lebanon, waɗanda suke nuna halin rashin ɗan’adamtaka na wannan gwamnatin azzaluma mai kashe yara, sun jawo baƙin ciki da damuwa mai tsanani.
Ana aikata wannan laifi ne tare da cikakken goyon bayan gwamnatin ta’addanci ta Amurka, da kuma shiru da wasu ƙasashen Larabawa da Musulmi suka yi, haka nan masu ikirarin kare haƙƙin bil’adama na ƙarya.
Ya zama dole dukkan Musulmi da masu neman ’yanci a duniya su dauki matsaya mai ƙarfi kan wannan ta’addanci da wannan laifi, su yi Allah-wadai da waɗannan hare-hare, sannan su bayyana cikakken goyon bayansu ga al’ummar Lebanon, musamman ga Hizbullah mai daraja, wadda ke ci gaba da kare ƙasa da al’ummar Lebanon cikin juriya da jarumtaka.
20 Ordibehesht 1405 (10 ga Mayu, 2026)
Husain Nuri Hamedani
Ra'ayinka